Toshe shafukan BATSA
Yadda Ake Toshe (Blocking) Na Haramtattun Website Na Batsa A Waya Idan baku manta ba, na sanar muku cewa, zan Koya Muku Hanyar Magance Wannan Matsala Ta Yadda Wayar Ku Bazata Taɓa Bude Shafukan Batsa Ba Na Internet. Lallai yana da kyau mu haɗu mu yaƙi kallace-kallacen Fina-Finan Batsa a tsakanin mu, domin Allah subhanahu wata'ala ya haramta, kuma yin hakan na jazawa ƙasa fitina da bala'i. A addinance dai kowa yasan kallon video na batsa haramunne, haka kuma kallonsu yana cutar da lafiyar idanu da kuma gurɓata zuciya tare da saka raunin imani da tsoron Allah a zukatan al'umma. Muna cikin wani zamani wanda yahudawa suke amfani da cigaban da aka samu na amfani da yanar gizo suna gurɓata mana tarbiyar ƙanne da yara dama mu kanmu ɗin baki ɗaya, ta hanyar buɗe website masu ɗauke da bidiyoyi na batsa wanda mu addininmu ya haramta mana kallansu, su kuma suna samun maƙudan ƙuɗaɗe ta haka. Ba'a iya maza kallon bidiyoyin batsa ya tsaya ba, harda mata kuma hakan yana 'daya dag...